Hasashe kan 'yan kwallo: Makomar Lacazette, White, Walker-Peters, Sancho, Wilson

Asalin hoton, Getty Images
Arsenal za ta sayar wa Atletico Madriddan wasan Faransa Alexandre Lacazette, mai shekara 29, a kan £30m da zarar dan wasan Gabon Pierre-Emerick Aubameyang, mai shekara 31, ya sabunta zamansa a kungiyar, a cewar jaridar Star Sunday
Ita kuma kuma jaridar Sky Sportsta ce Brighton ta ki sayar wa Leeds dan wasan Ingila mai shekara 22 Ben White a kan £22m. Dan wasan ya kwashe kakar wasan da ta wuce yana zaman aro a Elland Road.
Liverpool tana son dauko White, amma Chelsea ta shirya sayar da dan wasan Jamus Antonio Rudiger, mai shekara 27 don ta samu kudin sayen White. (Star Sunday)
Dan wasan Ingila Kyle Walker-Peters, dan shekara 23, yana dab da barin Tottenham bayan ya kulla yarjejeniya da Southampton a kan £12m, inda ya kwashe kakar wasan da ta wuce yana zaman aro. (Sunday Mirror)
Arsenal ta matsa kaimi na neman sabon gola domin maye gurbin Emiliano Martinez a yayin da take neman karin bayani kan tsawon lokacin da golanta Bernd Leno zai kwashe yana jinyar ciwon gwiwa. (Sun on Sunday)
Leicester da Liverpool sha'awar dan wasan Olympiakos da Girla Kostas Tsimikas, mai shekara 24, wanda za a sayar a kan £12m. (Mail on Sunday)
Borussia Dortmund za ta tayin sabunta kwangilar dan wasan Ingila Jadon Sancho, mai shekara 20, sannan ta kara masa alawis mai gwabi idan Manchester United ta gaza cika sharudan biyan £100m kan dan wasan zuwa ranar 10 ga watan Agusta. (Bild - in German)
Newcastle tana son dauko dan wasanBournemouth da Ingila Callum Wilson, mai shekara 28. (Mail on Sunday)
Daraktan wasanni na Bayer Leverkusen Rudi Voller ya gargadi Chelsea cewa kungiyarsa ba za ta sayar kan wasan Jamus Kai Havertz, mai shekara 21 kan kasa da £90m ba. (La Gazzetta dello Sport - in Italian)
Dan wasan Barcelona da Brazil Philippe Coutinho, mai shekara 28, wwanda a halin yanzu yake zaman aro aBayern Munich, ba zai yake hukunci kan makomarsa ba sai an kammala gasar Zakarun Turai ta bana. (Sport)
Arsenal tana son kashe £100m don dauko dan wasan Real Madrid Dani Ceballos, mai shekara 24, da dan wasan Atletico Madrid Thomas Partey, mai shekara 27, da kuma dan Lille Gabriel, mai shekara 22, a bazarar nan amma tana bukatar sayar da wasu 'yan wasa domin ta cika wannan buri nata. (Sun on Sunday)











