Kasuwar 'yan kwallo: Makomar Rice, Garcia, Havertz, Torreira, Sarr, Sessegnon, Tomori

Asalin hoton, EPA
Chelsea tana son tara £65m ta hanyar sayar da wasu 'yan wasanta da zummar samun kudin sayo dan wasanWest Hammai shekara21 dan kasar Ingila Declan Rice, in ji jaridar (Star).
Barcelona za ta ware £14m don sayo dan wasan Manchester City dan kasar Sufaniya mai shekara 19 Eric Garcia bayan ya gaya wa City ba zai sabunta kwangilarsa ba. (Goal)
Dan wasanBayer Leverkusendan kasar JamusKai Havertz, mai shekara 21, yana iya isaChelsea a makon gobe a kan £71m, yayin da Bayern Munich ta daina sha'awar daukarsa. (Star)
AC Milan na so dauko dan wasan Arsenal daUruguay Lucas Torreira, mai shekara 24, wanda aka daina damawa da shi a Emirates a karkashin jagorancin Mikel Arteta. (Telegraph - subscription required)
Dan wasanWatford da Senegal Ismaila Sarr, dan shekara 22, yana cikin 'yan kwallon da Liverpooltake son daukowa a bazara. (Liverpool Echo)
Ajax na son karbo aron dan wasan Tottenhamdan kasar Ingila Ryan Sessegnon, mai shekara 20. (Telegraph - subscription required)
Rennes ta soma tattaunawa da zummar dauko dan wasan Chelsea da Ingila mai shekara 22 Fikayo Tomori. (L'Equipe - in French)
Wolves za ta soma tattaunawa kan sabunta kwangilar kocinta Nuno Espirito Santo. (Mail)
Manchester United tana zawarcin golan Napoli da Italiya mai shekara 23 Alex Meret. (Star)
Everton tana son dauko dan wasan Atletico Madrid da Faransa Thomas Lemar. (Le10 Sport - in French)
Tottenham ta yi nisa a tattaunawar da take yi da Inter Milan domin dauko dan wasan Slovakia Milan Skriniar, wanda Liverpool da Manchester Unitedsuke zawarci. (Tuttosport via Sport Witness)
Leeds na duba yiwuwar kashe £15m don dauko dan wasanLiverpool da Wales mai shekara 23 Harry Wilson. (Sun)
Newcastle tana son kulla yarjejeniyar karbo aron Wilson, wanda ya kwashe kakar wasan da ta wuce yana zaman aro a Bournemouth, kuma tana son dauko dan wasanChelsea mai shekara 20 dan kasar Ingila Conor Gallagher. (Northern Echo)
Crystal Palace za ta fafata daFulham a yunkurin dauko dan wasan Southampton dan kasar Ingila Harrison Reed. Dan wasan mai shekara 25 ya kwashe kakar wasan da ta wuce yana zaman aro a Craven Cottage. (Football Insider)
Arsenal, Juventus da kuma Manchester City suna gogayya domin dauko dan wasan Lyon da Faransa mai shekara 22 Houssem Aouar. (L'Equipe via Mail)











