Kasuwar 'yan kwallo: Makomar Aubameyang, Willian, Lingard, Silva, Soyuncu, Rice, Terry

Pierre-Emerick Aubameyang

Asalin hoton, Getty Images

Dan wasan Arsenal da Gabon Pierre-Emerick Aubameyang, mai shekara 31, yana dab da sabunta kwangilar shekara uku a kungiyar. (Telegraph - subscription only)

Manchester United za ta karbi tayin sayar da dan wasanta mai shekara 27 dan kasar Ingila Jesse Lingard. (Guardian)

Lazio tana da kwarin gwiwar kammala sayen dan wasan Manchester City kuma tsohon dan wasan Sufaniya David Silva. Dan wasan mai shekara 34 zai shiga kasuwa a bazarar nan. (Sky Sports)

Dan wasanChelsea daBrazil Willian, mai shekara 31, amince da kwangilar shekara uku a Arsenal kuma za a rika ba shi £100,000 duk mako. (ESPN)

Barcelona za ta kashe euro 40m don dauko dan wasan Leicester mai shekara 24 dan kasar Turkiyya Caglar Soyuncu. (NTV Spor - in Turkish)

West Ham ba ta karbi wata bukata ba tadaukar dan wasan Ingila mai shekara21 Declan Rice, a cewar David Moyes. (Standard)

Tottenham za ta mayar da hankali wajen dauko dan wasan Bournemouth da Ingila mai shekara 28 Callum Wilson. (Express)

Mataimakin kocin Aston Villa John Terry na cikin jerin mutanen da ke neman zama kocin Bournemouth. (Metro)

Leeds ta ware £20m don dauko dan wasan Stuttgart mai shekara 22 dan kasar Argentina Nicolas Gonzalez. (Mirror)

Everton tana son dauko dan wasan Manchester Uniteddan kasar Portugal Diogo Dalot. (Star)

Manchester United ta so dauko dan wasan Netherlands Nathan Ake, mai shekara 25, kafin ya tafi Manchester City daga Bournemouth a makon da muke ciki.(Sky Sports)

Bournemouth ta ki amincewa da tayin £12m daSheffield United ta yi ba ta don daukogolan Ingila mai shekara 22 Aaron Ramsdale. (Sky Sports)

Arsenal ta sanya dan wasan Ingila Ainsley Maitland-Niles, mai shekara 22, a kasuwa. (Mirror)

Dan wasan Bayern Munich da Jamus Jerome Boateng ya ce ba "zai ki amsa tayin" komawa kungiyar da ke buga gasar Firimiya ba. Dan wasan mai shekara 31 ya kwashe kakar wasa ta 2010-11 a Manchester City. (Guardian).