Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Tottenham za ta ɗauko Hojbjerg, Greenwood zai sabunta zamansa a Manchester United
Zawarcin da Tottenham take yi na dan wasan Southampton dan kasar Denmark Pierre-Emile Hojbjerg, mai shekara 24, ya jefa dan wasan Ingila Harry Winks, mai shekara 24, cikin halin rashin tabbas a kungiyar. (Sunday Mirror)
Dan wasanManchester United dan kasar Ingila Mason Greenwood, dan shekara 18, zai rika karbar £40,000 duk mako a sabuwar kwangilarsa a Old Trafford - wata tara bayan ya sanya hannu kan kwangila a kungiyar. (Sun on Sunday)
Bristol City na son dauko mataimakin kocinAston Villa John Terry domin ya zama kocinta bayan mutumin da ta yi wa tayi tun da farko Steven Gerrard ya ki amsa tayinta. (Sunday Express)
Arsenal ta shirya biyan £40m domin dauko dan wasan Sporting Lisbon da ke buga gasar 'yan kasa da shekara 17 a Portugal Joelson Fernandes, dan shekara 17, wanda Barcelona da Juventus suke zawarcinsa. (A Bola - in Portuguese)
Har yanzu Chelsea ba ta yanke shawarar dauko Henderson ba. (Sunday Express)
Shugaban Leeds Angus Kinnear ya ce a makon gobe masu kungiyar za su gana da kocinta Marcelo Bielsa domin tattaunawa kan sabon kwantaragi da kuma batun musayar 'yan kwallo don su tunkari gasar Firimiya mai zuwa. (Sunday Express)
Zenit St Petersburg za ta biya £9m don dauko dan waan Liverpool Dejan Lovren, mai shekara 31, sai dai da alama Liverpool na son a biya ta kimanin £15m kan dan wasan na Croatia. (Mail on Sunday)
Villarreal ta tabbatar da cewa Santi Cazorla ba zai tsawaita zamansa a kungiyar ba, a yayin da ake rade radin cewa dan wasan na Sufaniya, mai shekara 35, zai iya komawa Arsenal a matsayin mai horas da 'yan wasa. (Sunday Mirror)
Borussia Dortmund ta sanya farashin £15m kan Jadon Sancho, mai shekara 20, amma dan wasan na Ingila, wanda ake hasashen zai tafi Manchester United, ya ki bayyana cewa zai bar kungiyar ta Jamus. (Sunday Express)
Manchester City tana tattaunawa da kungiyar Brazil Gremio domin dauko dan wasanta na tsakiya dan shekara 17 Diego Rosa a kan £4.5m. (Mail on Sunday).