An takawa Barca burki bayan lashe wasa 43 a gida a jere

Asalin hoton, Getty Images
Barcelona ta yi rashin nasara a gida a karon farko a La Liga, bayan cin karawa 43 a jere a gasar, inda Osasuna ta doke ta da ci 2-1 a Camp Nou ranar Alhamis.
Koda Barcelona ta yi nasara a kan Osasuna, ba zai hana Real Madrid lashe kofin La Liga da ta yi ba, bayan da ta doke Villareal da ci 2-1.
Jose Arnaiz ne ya fara ci wa Osasuna kwallo, kafin daga baya Lionel Messi ya farke a bugun tazara kuma na 23 da ya zura a raga a La Liga, shi ne kan gaba.
Osasuna ta karasa karawar da 'yan kwallo 10 a cikin fili, bayan da aka bai Enric Gallego jan kati,
Roberto Torres ne ya ci wa Osasuna kwallo na biyu a karin lokaci, bayan da Kike Barja ya buga masa kwallo ta je wajensa.
Rabonda Barca ta yi rashin nasara a gida tun Nuwambar 2018, bayan da Real Betis ta doke ta da ci 4-3.
Sakamakon wasannin mako na 37 a gasar La Liga ranar Alhamis.
- Eibar 3-1 Real Valladolid
- Athletic Bilbao 0-2 Leganes
- Barcelona 1-2 Osasuna
- Real Betis 1-2 Deportivo Alaves
- Celta Vigo 2-3 Levante
- Real Mallorca 1-2 Granada
- Real Madrid da Villarreal C
- Real Sociedad 0-0 Sevilla
- Valencia 1-0 Espanyol
- Getafe 0-2 Atletico Madrid
Wadanda ke kan gaba a cin kwallaye a gasar bana:
- Lionel Messi Barcelona 23
- Karim Benzema Real Madrid 21
- Gerard Moreno Villarreal 16
- Raul Garcia Athletic Bilbao 16
- Luis Suarez Barcelona 15
- Lucas Ocampos Sevilla 14
- Iago Aspas Celta de Vigo 14
- Alvaro Morata Atletico de Madrid 12
- Ante Budimir Real Mallorca 12
- Roger Marti Levante 11
- Willian Jose Real Sociedad 11
- Santi Cazorla Villarreal 11
- Lucas Perez Deportivo Alaves 11
- Jaime Mata Getafe 11
Wasannin mako na 38 da za a buga ranar 19 ga watan Yuli:
- Deportivo Alaves da Barcelona
- Atletico Madrid da Real Sociedad
- Espanyolda Celta Vigo
- Osasunada Real Mallorca
- Sevilla da Valencia C.F
- Real Valladolid da Real Betis
- Villarreal da Eibar
- Leganesda Real Madrid CF
- Levante da Getafe CF
- Granada da Athletic Bilbao
Jerin kungiyoyin da suka lashe La Liga:
- Real Madrid 34
- Barcelona 26
- Atletico Madrid 10
- Athletic Bilbao 8
- Valencia 6
- Real Sociedad 2
- Deportivo La Coruna 1
- Sevilla FC 1
- Real Betis 1
Kofin da Barca ta fatan dauka a bana shi ne na Champions League.
Barca za ta karbi bakuncin Napoli a karawar kungiyoyi 16 da suka rage a gasar ranar 8 ga watan Agusta.
A wasan farko sun tashi kunnen doki 1-1 a Italiya.











