Real Madrid ta lashe La Liga na bana kuma na 34 Jumulla

Asalin hoton, Getty Images
Real Madrid ta lashe kofin La Liga a karon farko tun bayan shekara uku, bayan da ta doke Villareal 2-1 a wasan mako na 37 da suka fafata ranar Alhamis a filin wasa na Alfredo Di Stefano.
Karim Benzema ne ya fara ci wa Madrid kwalon farko ta tsakanin kafar golan Villareal, Sergio Asenjo, sannanya ci na biyu a bugun fenariti da ya buga sau biyu, bayan takaddama.
Vicente Iborra ne ya zare daya amma hakan bai girgiza Madrid ba, wacce ta lashe kofin La Liga na bana kuma na 34 jumulla.
Kungiyar da Zinedine Zidane ke jan ragama ta ci dukkan karawa 10 da ta buga, tun bayan da aka ci gaba da wasannin shekarar nan.
Madrid za ta buga wasan mako na karshe na 38 a mataki na daya da tazarar maki bakwai tsakani nta da Barcelona wacce Osasuna ta doke ta 2-1 a Camp Nou.
Madrid wacce ta lashe dukkan karawar da ta buga, bayan da aka ci gaba da La Liga ta yi wasa 37 jumulla kawo yanzu.
Daga ciki ta yi nasara a guda 26 da canjaras 8 aka doke ta fafatawa uku ta kuma ci kwalloi 68 aka zura mata 23 a kakar bana.
Cikin watan Maris aka dakatar da wasannin La Liga don gudun yada cutar korona.
''Yan wasan Real Madrid da koci Zinedine Zidane ya fuskanci Villareal a filin wasa na Alfredo Di Stéfano.
Wadan da za su buga karawa da Villareal:
Masu tsaron raga: Courtois da Areola da kuma Altube.
Masu tsaron baya: Carvajal da Militão da Ramos da Varane da Nacho da kuma Mendy.
Masu wasan tsakiya: Kroos da Modric da Casemiro da Valverde da kuma Isco.
Masu cin kwallo: Hazard da Benzema da Bale da Lucas Vázquez da Jović da Asensio da Brahim da Mariano da Vinicius Jr. da kuma Rodrygo.
Sakamakon wasannin mako na 37 a gasar La Liga ranar Alhamis.
- Eibar 3-1 Real Valladolid
- Athletic Bilbao 0-2 Leganes
- Barcelona 1-2 Osasuna
- Real Betis 1-2 Deportivo Alaves
- Celta Vigo 2-3 Levante
- Real Mallorca 1-2 Granada
- Real Madrid da Villarreal C
- Real Sociedad 0-0 Sevilla
- Valencia 1-0 Espanyol
- Getafe 0-2 Atletico Madrid
Wadanda ke kan gaba a cin kwallaye a gasar bana:
- Lionel Messi Barcelona 23
- Karim Benzema Real Madrid 21
- Gerard Moreno Villarreal 16
- Raul Garcia Athletic Bilbao 16
- Luis Suarez Barcelona 15
- Lucas Ocampos Sevilla 14
- Iago Aspas Celta de Vigo 14
- Alvaro Morata Atletico de Madrid 12
- Ante Budimir Real Mallorca 12
- Roger Marti Levante 11
- Willian Jose Real Sociedad 11
- Santi Cazorla Villarreal 11
- Lucas Perez Deportivo Alaves 11
- Jaime Mata Getafe 11
Wasannin mako na 38 da za a buga ranar 19 ga watan Yuli:
- Deportivo Alaves da Barcelona
- Atletico Madrid da Real Sociedad
- Espanyolda Celta Vigo
- Osasunada Real Mallorca
- Sevilla da Valencia C.F
- Real Valladolid da Real Betis
- Villarreal da Eibar
- Leganesda Real Madrid CF
- Levante da Getafe CF
- Granada da Athletic Bilbao
Jerin kungiyoyin da suka lashe La Liga:
- Real Madrid 34
- Barcelona 26
- Atletico Madrid 10
- Athletic Bilbao 8
- Valencia 6
- Real Sociedad 2
- Deportivo La Coruna 1
- Sevilla FC 1
- Real Betis 1











