Liverpool za ta daga kofin Premier bayan karawa da Chelsea

Asalin hoton, Getty Images
Liverpool za ta daga kofin Premier League na bana da ta lashe a Anfield, bayan ta buga karawa da Chelsea ranar Laraba.
Kungiyar ta anfield za ta yi bikin daga kofin da ta lashe a wurin zaman 'yan kallo a filinta da ake kira Spion Kop ko kuma Kop a takaice.
Liverpool ta lasshe Premier League na bana ne a karon farko tun bayan shekara 30 kuma na 19 jumulla tun saura wasa bakwai-bakwai a karkare kakar bana.
Sai dai magoya bayan kungiyar ba za su halarci bikin daga kofin ba, sakamakon cutar Korona.
Amma dai za a nuna bikin a talabijin kyauta, kuma tsohon zakakurin kungiyar, Kenny Dalglish ne zai bai wa 'yan wasa lambar girma a lokacin.
Kyaftin din Liverpool, Jordan Henderson shi ne zai daga kofin duk da jinya da yake yi yanzu hakan.
Kocin Liverpool, Jurgen Klopp ya fayyace cewar Henderson - wanda ya daga musu Champions League a bara - zai kasance kyaftin din kungiyar na farko da zai daga kofin Premier League tun bayan Alan Hansen da ya yi a 1990, duk da Henderson na fama da jinyar rauni a kakar bana.
Henderson da sauran 'yan wasan Liverpool za su daga kofin a wurin da aka kawata da wani kyalle mai girma da magoya baya suka tanada a tsakiyar wajen zaman 'yan kallo da ake kira Kop Stand.
Liverpool ta bukaci magoya bayanta da su zauna a gida su kalli bikin a talabijin don hana yada cutar korona.











