Arsenal ta yi wa Liverpool fancalen hada maki 100 a Premier

Asalin hoton, Getty Images
Arsenal ta yi nasarar doke Liverpool da ci 2-1 a wasan mako na 36 a gasar Premier League da suka fafata a Emirates ranar Laraba.
Sadio Mane ne ya fara ci wa Liverpool kwallo, sai dai Gunners ta farke ta hannun Alexandre Lacazette a minti na 32.
Arsenal ta kara na biyu daf da za su je hutu ta hannun Reiss Nelson, wanda hakan ya sa ta hada maki ukun da take bukata a karawar.
Da wannan sakamakon Arsenal ta yi wa Liverpool fancalen hada maki 100 da take fatan doke tarhin da Manchester City ta kafa a gasar ta Premier League.
Liverpool tana nan a matakinta na daya a kan teburi da maki 93, kuma ko da za ta yi nasara a fafatawa biyun da suka rage za ta hada maki 99 ne.
Tun saura wasa bakwai-bakwai a karkare kakar bana, Liverpool ta lashe Premier League na bana, kuma a karon farko tun bayan shekara 30, kuma na 19 jumulla.
Arsenal wacce take neman gurbin shiga gasar Zakarun Turai ta Europa League ta badi tana nan a mataki na tara a kan teburi da maki 53.
Rabon da Arsenal ta yi nasara a kan Liverpool a gasar Premier League tun 4-1 da ta ci a Emirates a Afirilun 2015.
Liverpool wacce ta buga wasa 36 ta yi nasara a 30 da canjaras uku kuma karo na uku da aka doke ta a wasannin bana a Premier League.
Wannan ne karo na uku da kungiyoyin suka yi gumurzu a tsakaninsu a bana, bayan da Liverpool ta doke Arsenal 3-1 a Anfield a gasar Premier ranar 24 ga watan Agustan 2019.
Haka kuma sun fafata ranar 30 ga watan Oktoban 2019 a Caraboa Cup, inda suka tashi 5-5, kuma Liverpool ta kai zagayen gaba, bayan doke Arsenal 5-4 a bugun fenariti.
Liverpool za ta yi bikin daga kofin Premier League na bana a makon gobe, bayan ta kara da Chelsea a Anfield a gasar Premier wasan mako na 37.
Arsenal za ta ziyarci Aston Villa ranar 21 a wasan mako na 37 a Premier League, yayin da ranar 22 ga wata Chelsea za ta ziyarci Liverpool a Anfield.
Karawa tsakanin Arsenal da Liverpool:
Arsenal ba ta yi nasara a kan Liverpool a wasa tara baya ba tun 4-1 da ta ci a Emirates a Afirilun 2015 (ta yi canjaras hudu aka doke ta karawa biyar).
Liverpool ta zura kwallo 90 a ragar Gunners a gasar Premier League, kuma kungiya daya da ta sharara mata kwallaye da yawa a gasar.
Batutuwan da suka shafi Arsenal:
Rashin nasara da Arsenal ta yi a hannun Tottenham ya kawo karshen cin wasa hudu da kungiyar ta yi.
Watakila Gunners ta hada maki 59 a kakar bana a Premier League, maki mafi karanci da za ta hada kenan bayan buga wasa 38.
Wasa daya kacal Arsenal ta yi nasara a kungiyoyi shida da ke kan teburin bana.
Arsenal ta barar da maki 15 da ya kamata ta hada tun daga lokacin da Mikel Arteta ya karbi aiki a cikin watan Disamba.
Alexandre Lacazette ya ci kwallo biyu a wasa uku baya, sun kuma yi yawan wadanda ya zura a raga a wasa 14 da ya buga.
Batutuwan da suka shafi Liverpool:
Liverpool na bukatar wasa uku da suka rage mata domin haura maki 100 da Manchester City ke rike da tarihi a Premier League points.
Za kuma ta iya kafa tarihin lashe wasa 31 a bana a Premier League idan ta doke Arsenal.
Liverpool ta ci wasa biyar a Premier League a Landan har da wasa hudu a kakar bana.
Arsenal ta yi nasarar doke kungiyoyin Landan a kakar 1933 a lokacin Arsenal da Chelsea ne ta doke su.
Arsenal ba ta doke Jurgen Klopp ba a wasa takwas a Premier League wanda ya ci wasa biyar da canjaras uku, kuma Liverpool ta zura kwallo 26 a wadan nan karawar.











