Coronavirus: Na yi kewar rungumar mutanen da nake kauna - Mikel Arteta

Mikel Arteta

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Mikel Arteta ya zama kocin Arsenal a watan Disamba

Ya kamata mutane "su fito fili su fadi halin da suka shiga ciki" kan annobar coronavirus, a cewar kocin Arsenal Mikel Arteta bayan ya warke daga cutar.

Arteta, mai shekara 38, ya kamu da cutar ranar 12 ga watan Maris sai dai ya warke daga cutar bayan ya killace kansa.

"Muna cikin duniyar da komai yana cikin shafukan sada zumunta, komai an tura shi a matsayin sakon WhatsApp," in ji dan kasar ta Spain.

"Amma kun san muhimmancin taba juna da rungume juna?

"Na yi kewar rungumar mutanen da nake kauna

"Ya kamata mu fito fili mu fadi irin halin da muka shiga. Ya dace mu gaya wa juna yadda muke ji."

Arteta ya bayyana cewa ba ya jin dadin jikinsa bayan an tabbatar cewa Evangelos Marinakis - mamallakin kungiyar kwallon kafar Olympiakos, wadanda suka fafata da Arsenal a gasar Europa League a watan Fabrairu - ya kamu da coronavirus ranar 10 ga watan Maris

Ranar Alhamis, Arteta ya ce ya "warke sarai" sannan ya bukaci mutane su yi biyayya ga umarnin gwamnati na zaunawa a gidajensu.

"Wannan wata cuta ce da ta jefa duniya cikin rudani kuma tana sauya abubuwan da suka kamata mu bai wa muhimmanci a rayuwa. Don haka ya kamata mu dauki darasi a kanta," in ji Arteta a tataunawarsa da shafin intanet na Arsenal

A farkon mako ne ya kamata 'yan wasan Arsenal su koma atisaye bayan sun kammala killace kansu na mako biyu, ama an jinkirta komawar su.

Arteta ya ce babban abin da ya jefa shi cikin damuwa shi ne matsayin 'ya'yansa uku bayan matarsa da 'yar aikinsu sun kamu da coronavirus.

Arteta ya killace kansa a wani daki da kuma bandaki tsawon kwana biyu zuwa uku amma matarsa ta kwanta rashin lafiya jim kadan bayan hakan.