Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Arteta ya damu da rashin isassun kudi da Arsenal za ta yi cefane mai albarka
Mikel Arteta " bai da tabbaci ko" zai samu kudin da zai bunkasa 'yan kwallon Arsenal ta yadda za su kalubalanci abokan hamayyarsu a harkar kwallon kafa.
Gunners ta yi nasarar doke Liverpool 2-1 ranar Laraba, wacce ta lashe kofin Premier League na bana, sai dai Arsenal na da jan aikin samun gurbin shiga gasar Zakarun Turai ta badi.
Arsenal din tana ta tara a kan teburi da maki 53 da tazarar maki uku tsakaninta da ta shida Wolverhampton.
An tambayi kocin ko zai samu kudin da zai sayo 'yan wasa a badi? sai ya ce bai sani ba a hira da ya yi da Sky Sports: ''Abin damuwa ne da ke raina.''
Ya kara da cewar ''Kana bukatar karfafa kungiya da kwararrun 'yan wasa, ba wani tsafi bane. Ya kamata mu bunkasa kungiya da shahararru kuma fitattun 'yan kwallo da za a gwabza da su a manyan wasa.''
Arsenal ta kashe sama da fam miliyan 135 a kakar bara har da sayen dan kwallo mafi tsada a kungiyar da ta dauki Nicholas Pepe kan fam miliyan 72 da Kieran Tierney kan fam miliyan 25.
Sauran da ta saya sun hada da David Luiz da Gabriel Martinelli da kuma William Saliba - wanda ya koma Emirates domin buga wasannin aro daga Saint-Etienne.
Sai dai duk da wannan cefanen, Arsenal ta kasa shiga cikin 'yan hudun farko a teburin Premier League na bana, kuma a cikin watan Nuwamba Gunners ta sallami Unai Emery.