Arsenal ba ta motsa a matakinta a teburin Premier ba

Jamie Vardy

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Vardy ne kan gaba a cin kwallaye a gasar Premier League mai guda 22 a raga

Arsenal ta tashi 1-1 da Leicester City a wasan mako na 34 a gasar Premier League da suka fafata ranar Talata a Emirtaes.

Gunners ce ta fara cin kwallo ta hannun Pierre-Emerick Aubameyang, kuma na 20 da ya zura a raga a kakar bana tun kan su je hutu a karawar.

Mai tsaron ragar Leicester Ciry, Kasper Schmeichel ya hana Arsenal ta kara zura masa kwallo, inda ya tare damar da Alexandre Lacazette da ta Bukayo Saka da suka samu.

Arsenal ta koma buga karawar da 'yan kwallo 10 a cikin fili, bayan da aka bai wa Eddie Nketiah jan kati saura minti 15 a tashi daga fafatawar.

An kori Nketiah wanda ya canji dan wasa minti hudu da shiga fili, bisa ketar da ya yi wa James Justin.

Leicester ta farke kwallo ta hannun Vardy, bayan da Demaray Gray ya buga kwallo ta je wajensa saura minti hudu a tashi wasa.

Sai da alkalin wasa ya tuntubi na'urar da ke taimaka masa yanke hukunci wato VAR wacce ta ce Vardy bai yi satar gida ba.

Vardy ya ci kwallo 22 kenan a gasar Premier League ta shekarar nan da tazarar guda biyu tsakaninsa da dan wasan Arsenal, Aubameyang mai 20 a raga.

Da wannan sakamakon Gunners ta samu karin maki daya tal, amma tana nan a matakinta na bakwai a teburi da take fatan samun gurbin buga gasar zakarun Turai ta badi.

Ita kuwa Leicester City ta yi kasa zuwa mataki na hudu, bayan da Chelsea ta maye gurbinta, sakamakon doke Crystal Palace 3-2 da ta yi a ranar Talata.