Sabani tsakanin Lloris da Son abu ne mai kyau - Mourinho

Asalin hoton, EPA
Kocin Tottenham, Jose Mourinho ya ce dan sabanin da aka samu tsakanin kyaftin Hugo Lloris da Son Heung-min a karawa da Everton abu ne mai kyau.
Kyaftin Lloris ne ya je ya dafa bayan Son ya kuma ture shi lamarin da ya bai wa dan kwallon tawagar Korea ta Kudu haushi ya juyo a fusace sai abokin wasansu ya shiga tsakani.
Daga nan suka shiga dakin hutun 'yan wasa, bayan da alkalin wasa ya hura usur domin su sha ruwa su huta kan wasan zango na biyu.
Sai dai kuma bayan da aka tashi wasan Premier League da suka yi nasara a kan Everton da ci 1-0, 'yan kwallon biyu sun gaisa sun kuma rungumi juna.
Bayan da aka tashi wasan sai Lloris ya ce ''Babu wata matsala a tsakaninsu''.
'Yan wasan biyu sun kusan bai wa hammata iska, bayan da Lloris ya ture Son da cewar mai ya sa bai dawo ya tare baya ba ya hana dan wasan Everton, Richarlison gwada raga.
Nasarar da Tottenham ta yi ya sa Mourinho ya ci wasa na 200 a gasar Premier League, kuma shi ne na biyar a jerin masu horarwa da suka yi wannan bajintar.
Tottenham ta yi nasarar ce, bayan da Sheffield ta doke ta 3-1 kafin karawa da Everton, kuma kungiyar tana ta takwas a teburin Premier League na bana.











