Nemanja Matic zai ci gaba da zama a Manchester United zuwa 2023

Asalin hoton, Reuters
Dan kwallon Manchester United, Nemanja Matic ya tsawaita kwantiraginsa da kungiyar zuwa karshen kakar 2023.
Dan wasan tawagar Serbia, mai shekara 31 ya koma United daga Chelsea a 2017 wanda yarjejeniyarsa zai kare a Old Trafford a karshen Yunin 2021.
Ole Gunnar Solskjaer ya ce ''Ya yi murna da Matic zai ci gaba da taka leda a United, na san kwarewarsa da iya jagorancinsa zai taimaka wajen bunkasa matasan 'yan kwallon da muke da su.''
"Nemanja yana kaka ta uku a Old Trafford kawo yanzu, ya kuma san mahimmacin buga wa Manchester United kwallo da kare martabarta."
Matic ya yi wa United wasa 27 a dukkan fafatawa a kakar bana.
Kungiyar ta Solskjaer ba ta yi rashin nasara a wasa ba tun daga watan Janairu - karawa 16 kenan a jere a dukkan fafatawar da ta buga - tana ta biyar a kan teburin Premier League na bana..
Haka kuma United ta kai wasan daf da karshe a FA Cup a bana tana kuma cikin gasar zakarun Turai ta Europa League.







