Har yanzu Barca ba ta fitar da ran lashe La Liga ba

Antoine Griezmann

Asalin hoton, Reuters

Barcelona ta ci gaba da sa kaimi na ganin ta kare kofin La Liga da take da shi, bayan da ta doke Villareal 4-1 a karawar da suka yi ranar Lahadi.

Villareal ce ta fara cin kanta ta hannun Torres daga baya Luis Suarez ya ci na biyu sai Antoine Griezmann da ya zura na uku, matashin dan wasa Ansu Fati ya kara na hudu.

Villareal ta ci kwallonta ta hannun Moreno tun a minti na 14 da take leda.

'Yan gaban Barcelona uku Messi da Suarez da kuma Griezmann sun taka rawa mai kayatarwa a daya daga wasan da suka yi mai kyau a tsakaninsu.

Messi wanda shi ne ya bai wa Suarez da Grizman kwallayen da suka ci, kawo yanzu ya bayar da 19 da aka zura a raga a gasar La Liga ta bana.

Barca wacce take ta biyu da tazarar maki hudu tsakaninta da Real ta daya kuma saura wasa hudu-hudu a karkare karawar bana na fatan Madrid ta yi sake a sauran karawarta.

Villareal ta ci karawa biyar da canjaras daya tun da aka ci gaba da gasar La Liga ta shekarar nan, wacce aka dakatae saboda gudun yada cutar korona.