Adam ya ci Man City inda Southampton ta hada maki uku

Che Adams

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Kwallon farko da Che Adams ya ci a gasar Premier League

Che Adams ne ya ci wa Southampton kwallonsa na farko a gasar Premier League da ya bai wa kungiyar maki uku, bayan doke Manchester City 1-0 a St Mary.

Adam, wanda ya koma Saints daga Birmingham City kan fam miliyan 15 ya ci kwallon tun daga yadi na 40, inda ya daga kwallon, bayan da ya tabbatar Ederson baya cikin raga.

Manchester City ta buga karawar da sauyin 'yan kwallo shida daga wadanda suka ci Liverpool 4-0 a ranar Alhamis a Etihad.

Kwallon da aka ci City ya sa kungiyar ta sa matsi matuka ga Saints, inda Fernandinho ya buga kwallo ta bugi turke da wadda David Silver ya sa kai amma gola Alex McCartthy ya tsare raga gam.

Ita ma Southampton ta samu damarmaki duk da matsi da City ta saka mata, inda Nathan Redmond da Danny Ings da kuma Stuart Armstrong suka barar da kwallaye.

City wacce take ta biyu a teburin bana biye da Liverpool wacce ta lashe kofin Premier na bana ta bai wa City tazarar maki 23, bayan da ta ci Aston Villa 2-0 ranar Lahadi.