Liverpool ta kara nutsa Villa cikin 'yan kasan teburi

Sadio Mane of Liverpool scores against Aston Villa

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Sadio Mane ne ya fara ci wa Liverpool kwallon farko a minti na 71

Liverpool ta ci wasa na farko tun bayan da ta lashe kofin Premier na bana, bayan da ta doke Aston Villa da ci 2-0 a Anfield.

Liverpool wacce ta sha kashi a hannun Manchester City da ci 4-0 a Etihad ranar Alhamis ta fara cin Aston Villa ta hannun Sadio Mane.

Aston Villa ta samu damarmaki da yawa, kuma ta yi ta kokarin fara cin kwallo a karo da dama, sai dai hakan bai yi wu ba.

Kungiyar ta Anfield ta kara kwallo na biyu ne ta hannun Curtis Jones kuma na farko da ya ci a Premier, wanda kwanan nan ya sa hannu kan yarjejeniyar ci gaba da taka leda a kungiyar.

Da wannan nasarar Liverpool ta ci wasa 17 a gasar Premier da ta buga a gida a bana,

Ita kuwa Aston Villa da ta yi rashin nasara tana mataki na 18 a kasan teburi, kuma har yanzu ba ta ci wasa ba tun da aka ci gaba da fafatawar Premier League ta shekarar nan.

Kawo yanzu Liverpool ta hada maki 89 daga wasa 33 da ta yi a kakar nan, za kuma ta iya haura tarihin da Man City ta kafa na samun maki 100.

Saura wasa biyar a karkare kakar shekarar nan, saboda haka Liverpool na bukatar lashe karawar da suka rage kenan.

Shekara 128 da ta gabata Sunderland ke rike da tarihin yawan hada maki da yawa a gida, bayan da ta lashe dukkan fafatawar da ta buga a kakar.