Real Madrid ta ci wasa 350 tare da Marcelo

Asalin hoton, Real Madrid FC
Ranar Lahadi Real Madrid ta yi nasara a kan Athletic Bilbao a gasar La Liga, kuma shi ne na 350 da Marcelo aka yi nasara tare da shi.
Kuma Marcelo wanda ya buga karawa 509 ne aka yi wa ketar da Real ta samu fenariti, wanda kyaftin Sergio Ramos ya buga ya kuma ci kwallon.
Bayan da aka tashi wasan da Real ta doke Athletic Bilbao, shugaban Madrid, Florentino Pérez ya bai wa Marcelona rigar girmamawa ta nasara 350 a kungiyar.
Marcelo mataimakin kyaftin ya fara buga wa Real Madrid wasa ranar 7 ga watan Janairun 2007 a karawa da Deportivo.
Dan kwallon tawagar Brazil ya lashe kofi 21 a kungiyar ta Santiago Bernabeu ciki har da Champions Leagues hudu da kofin zakarun nahiyoyin duniya hudu.
Sauran sun hada da European Super Cups uku da La Liga hudu da Copas del Rey biyu da kuma Spanish Super Cup hudu.
Marcelo ya yi wa Real Madrid wasa 509 yana kuma kaka ta 14 a Santiago Bernabeu.
Wasanni 350 da aka yi nasara da Marcelo a Real Madrid sun hada da La Liga sau 248 da cin karawar Champions League 65 da kuma 22 a fafatawar Copa del Rey.
Haka kuma Real Madrid ta ci wasa tare da Marcelo a gasar kofin duniya na zakarun nahiyoyi sau takwas da European Super Cup sau uku da nasara hudu a Spanish Super Cup.
Real Madrid tana mataki na daya a kan teburin La Liga na bana da maki 77.
Barcelona ce mai rike da kofin bara ke mataki na biyu da tazarar maki hudu tsakaninta da Real Madrid











