Guardiola na fatan City za ta buga Champions League a badi

Kocin Manchester City, Pep Guardiola na sa ran za suyi nasara a daukaka kakar hukuncin da Uefa ta dakatar da su daga shiga gasar zakarrun Turai kaka biyu.

City ce ta daukaka kara a kotun sauraren kararrakin wasanni ta duniya, kuma ranar 13 ga watan Yuni ake sa ran sanar da sakamako.

Guardiola ya ce ''A shirye muke''

''Ina cike da kwarin gwiwa da amannar cewar mutanen za su amince mu buga Champions League a badi, kuma muna son buga wasanni a shekarun hukuncin da aka yi mana.''

An hukunta City ne da cin kungiyar tarar fam miliyan 25, bayan da Uefa ta sameta da laifin karya ka'idar lasisi da kuma ta kashe kudi bisa ka'ida.

Guardiola ya kara da cewar ''Ranar 13 ga watan Yuli za mu san makomarmu.''

City tana cikin kungiyoyin da ke buga Champions League na bana wanda za a ci gaba da wasanni a cikin watan Agusta.

Kungiyar ta Etihad ta yi nasarar doke Real Madrid da ci 2-1 a Santiago Bernabeu a wasan farko na kungiyoyi 16 da suka rage a fafatawar.

A ranar Alhamis City ta zazzagawa Liverpool kwallo 4-0 wacce ta lashe kofin Premier League na shekarar nan saura karawa bakwai-bakwai a kammala wasannin bana.