Manchester City da Chelsea na zawarcin Chilwell

Manchester City ta shirya yin gogayya da Chelsea a yunkurin dauko dan wasan Leicester City mai shekara 23 dan kasar Ingila, Ben Chilwell, idan kwangilarsa ta kare, a cewar jaridar Telegraph.)

Napoli ba za ta rage farashin dan wasan Senegal dan shekara 28 Kalidou Koulibaly daga £100m ba, duk da matsalar rashin kudin da kungiyoyi ke ciki sakamakon cutar korona. Ana rade radin dan wasan zai koma Manchester United. (Mirror)

Manchester United da Real Madrid suna sanya ido kan halin da dan wasan Inter Milan dan kasar Argentina Lautaro Martinez, mai shekara 22, yake ciki bayan yunkurinsa na komawa Barcelona ya ci tura. (Marca via Mirror)

Dan wasan Juventus dan kasar Bosnia-Herzegovina Miralem Pjanic, mai shekara 30, ya yi watsi da tayin da Chelsea da Paris St-Germain suka yi masa na komawa daya daga cikinsu saboda yana son komawa Barcelona. (Marca)

Tottenham ta janye daga yunkurin da take yi na dauko dan wasan tsakiya na Italiya mai shekara 20, Nicolo Zaniolo saboda kudi £62m da Roma ta sanya a kansa. (Star)

Kocin Celtic Neil Lennon ya ce kungiyar tana tattaunawa domin sabunta kwantaragin dan wasan Faransa mai shekara 24 Odsonne Edouard, wanda ake cewa zai koma Arsenal ko Manchester United.(Mail)

Dan wasan Spaniya Angelino, dan shekara 23, ya shirya tsaf domin komawa Manchester City bayan zaman aron da yake yi a RB Leipzig, wacce ta kasa biyan £25m a kansa. . (Manchester Evening News)

Tsohon dan wasan Chelsea Michael Ballack ya goyi bayan matakin sayo dan wasan Jamus mai shekara 24 Timo Werner daga RB Leipzig yana mai cewa ya yi amannar nan da nan dan wasan zai nakalci yadda ake wasa a Premier League. (Sky Germany)

Dan wasan tsakiya na Croatia Ivan Rakitic, mai shekara 32, yana da niyyar ci gaba da zama a Barcelona har lokacin da kwangilarsa za ta kare a karshen bazara ta 2021 duk da rahotannin da ke cewa zai bar kungiyar nan ba da dadewa ba (Goal)

Dan wasan Paris St-Germain Ander Herrera, mai shekara 30, ya ce abokin wasansa dan kasar Uruguay Edinson Cavani, wanda kwangilarsa za ta kare a bazara, yana son buga tamaula a Spaniya. Ana rade radin Cavani, mai shekara 33, zai koma Atletico Madrid (Diario As via Mail)

Manyan kungiyoyi suna fafatawa don dauko dan wasan Manchester United dan shekara 19 Brandon Williams. (Mirror)