Ronaldo ya zama na farko mai kwallo 25 a kakar Serie A tun 1961

Cristiano Ronaldo

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Sai da Cristiano Ronaldo ya kusan cinye kaka biyu kafin ya ci wa Juventus kwallo a bugun tazara

Juventus ta doke Torino da ci 4-1, kuma Cristiano Ronaldo ya zama na farko da ya ci wa kungiyar kwallo 25 a kakar Serie A, tun bayan 1961.

A wasan na hamayya da aka doke Torino, Gianluigi Buffon ya kafa tarihin yawan buga wasannin Serie A mai 648.

Paulo Dybala ne ya fara ci wa Juventus na farko, sai Ronaldo da ya bai wa Juan Cuadrado kwallo ya zura na biyu a raga.

Daga nan Torino ta zare daya ta hannun Andrea Belotti, nan da nan Ronaldo ya ci wa Juventus kwallo na uku a bugun tazara, bayan da Torino ta ci.

Kawo yanzu Ronaldo ya ci kwallo a bugun tazara sau 46 a karawar da ya yi a kungiya, inda 32 a Real Madrid da kuma 13 a Manchester United da daya a Juventus.

Ya kuma zama na farko da ya ci kwallo 25 a kakar Serie A tun bayan Omar Sivori da ya yi wannan bajintar a kakar 1960-61.

Shi kuwa Buffon ya yi wasa na 648 a babbar gasar kwallon kafar Italiya ya kuma haura Paolo Maldini mai tarihin yawan buga gasar.

Buffon, mai shekara 42, ya samu damar kafa yawan buga gasar Serie A, bayan da ya ci gaba da kama gola a wasannin bana, kuma tun Disamba ya yi ta dakon hakan.

Idan ka hada da wasa 17 da ya buga a Paris St-Germain a gasar Faransa a bara, Buffon shi ne kan gaba a yawan buga wasanni a manyan gasar Turai ta kasashe biyar wanda keda 665.

Gareth Barry, wanda ke taka leda a West Brom yanzu haka a gasar Championship,ya yi wasa 653 a gasar Premier League.

Juventus wacce ke fatan lashe kofin Serie A na tara a jere ta bai wa Lazio tazarar maki bakwai wacce za ta karbi bakuncin AC Milan idan anjima.