'Yan Barca da ta je Villareal buga gasar La Liga da su

Asalin hoton, La Liga Santander Twitter
Barcelona za ta kara da Villareal a wasan mako na 34 a gasar cin kofin La Liga da za su fafata a Estadio de la Ceràmica ranar Lahadi.
A wasan farko da suka fafata a Camp Nou ranar 24 ga watan Satumbar 2019, Barcelona ce ta yi nasara da ci 2-1.
Kuma tun kan hutu Barca ta ci kwallayenta ta hannun Antoine Griezmann da kuma Arthur, yayin da Santi Cazorla ya zare wa Villareal kwallo daf da hutu.
Barcelona wacce Real Madrid ta bai wa tazarar maki hudu tana ta biyu da maki 70, ita kuwa Villareal mai maki 54 tana ta biyar a teburin bana.
Tun a ranar Asabar Barcelona ta kammala atisaye ta kuma bayyana 'yan kwallon da za ta je da su Villareal har da matasan 'yan wasanta a ciki.
Matasan masu buga wa karamar kungiyar Barca da ta gayyata sun hada da Inaki Peña da Riqui Puig da Collado da Ansu Fati da R. Araujo da Morer da Monchu da kuma J. Cuenca.
Manyan 'yan wasa da koci Quique Setién ya bayyana da za su fuskanci Villareal ranar Lahadi sun hada da Ter Stegen da N. Semedo da Piqué da I. Rakitic da kuma Sergio.
Sauran sun hada da Arthur da Suárez da Messi da Neto da Lenglet da Griezmann da Jordi Alba da Braithwaite da S. Roberto da Vidal da kuma Junior.
'Yan wasan Barcelona da ke jinya sun hada da Ousmane Dembélé da Frenkie De Jong da kuma Samuel Umtiti.











