Inter Milan ta dauko Achraf Hakimi daga Real Madrid

Achraf Hakimi

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Achraf Hakimi ya nuna kwarewarsa a lokacin da yake wasannin aro a Borussia Dortmund

Inter Milan ta dauki mai tsaron baya, Achraf Hakimi daga Real Madrid kan yarjejeniyar shekara biyar.

Dan wasan tawagar Morocco mai shekara 22 ya buga wa Real Madrid wasa 17, yi kaka biyu a wasannin aro a Borussia Dortmund.

Wasu rahotanni na cewa Inter ta biya Real Madrid kudin da ya kai fam miliyan 36 ga dan wasan da ya fara wasa daga makarantar koyon tamaula ta Real Madrid.

A wata sanarwa da Real Madrid ta fitar ta yi godiya ga Hakim kan gudunmuwar da ya bayar ta kuma yi masa fatan alheri a sabuwar kungiyar da ya koma.

Hakimi mai tsaron baya ko daga hagu ko dama yana kuma iya wasa a tskaita an nuna hotonsa a lokacin da litkitocin Inter Milan ke gwada lafiyarsa.

Ya buga wa Dortmund wasa sama da 70 ya kuma ci kwallo 12.