Bukayo Saka ya sa hannu kan yarjejeniyar ci gaba da zama a Arsenal

Asalin hoton, Getty Images
Dan wasan tawagar kwallon kafa ta Ingila ta 'yan shekara 18, Bukayo Saka ya sa hannu kan yarjejeniyar ci gaba da wasa a Arsenal.
Mai shekara 18 ya fara buga wa babbar kungiyar Arsenal kwallo a kakar bana ya kuma buga wasnni.
Tun farko yarjejeniyarsa zai kare a Gunners a karshen kakar bana, hakan ya sa ake cewar zai bar Emirates.
Dan kwallon na tsaron baya daga hagu ya kan kuma yi wasa daga dama.
Arsenal za ta karbi bakuncin Norwich City a gasar Premier League ranar Laraba.
Arsenal tana mataki na 10 a kan teburin bana, yayin da Norwich City ke mataki na 20.






