Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Sane ya rattaba kwantiragi da Bayern Munich
Leroy Sane ya ce Bayern Munich babbar kungiya ce mai manyan buri a wani jawabi da ya yi bayan da ya koma Jamus daga Manchester City.
Dan kwallon tawagar Jamus, mai shekara 24 ya koma Bayern daga Manchester City kan fam miliyan 44.7 zai iya kai wa fam miliyan 54.8 karin tsarabe-tsarabe.
Sane ya koma City daga Schalke a shekarar 2016 kan fam miliyan 37, ya kuma lashe Premier League da FA Cup da kuma League Cup biyu.
Dan wasan ya buga karawar Premier League 135 ya kuma ci kwallo 39 ya bayar da 45 aka zura a raga.
Sane wanda ya buga wa tawagar Jamus wasa 21 zai fara atisaye a Bayern Munich a makon gobe, sai dai ba zai buga mata Champions League na bana ba.