Ko Messi zai ci kwallo na 700 a karawa da Atletico Madrid?

Asalin hoton, Getty Images
Barcelona za ta karbi bakuncin Atletico Madrid a gasar La Liga a daya daga wasan da ake gani zai yi zafi a ranar Talata.
Kyaftin Lionel Messi ya ci kwallo 699 a Barcelona da guda 70 da ya ci wa tawagar kwallon kafa ta Argentina.
Messi ya ci kwallo 26 a wasa 36 da ya yi a kakar bana har da 21 da ya zura a raga a gasar La Liga.
Sai dai kuma rabon da kyaftin din Argentina ya ci wa Barcelona kwallo tun wadda ya zura a ragar Leganes ranar 16 ga watan Yuni.
A wasan farko da suka fafata ranar 1 ga watan Disambar 2019, Barcelona ce ta yi nasara da ci 1-0 a gidan Atletico kuma Lionel Messi ne ya ci kwallo,
Barcelona tana mataki na biyu a kan teburi da maki 69 da tazarar maki biyu tsakaninta da Real Madrid mai jan ragamar teburin La Liga na bana.
Ita kuwa Atletico tana matsayi na uku a teburin da maki 58, tana kuma taka rawar gani tun lokacin da aka ci gaba da La Liga ta shekarar nan.
Atletico ta ci wasa hudu daga biyar da ta fafata, ita kuwa Barcelona ta yi canjaras biyu da ya sa ta rasa matakinta na daya a kan teburi.
Idan Barcelona ta doke Atletico za ta hau kan teburi da tazarar maki daya kan Real Madrid ta buga wasanta da Getafe a gida ranar Alhamis.
Tuni kocin Barcelona Quique Satien ya bayyana 'yan wasa 23 da za su fuskanci Atletico.
Sergio Busquets zai koma buga wa Barca wasanni bayan da ya kammala dakatarwar da aka yi masa shi kuwa Sergi Roberto ya warke daga jinya.
'Yan wasan Barcelona da za su fuskanci Atletico Madrid:
Ter Stegen da N. Semedo da Piqué da I. Rakitic da Sergio da Arthur da Suárez da Messi da Neto a Lenglet da Griezmann da Jordi Alba da Braithwaite da kuma S. Roberto.
Sauran sun hada da Vidal da Umtiti da Junior da Iñaki Peña da Riqui Puig da Collado da Ansu Fati da R. Araujo da kuma Monchu.
Har yanzu Dembélé da kuma De Jong na jinya.











