Mario Gomez ya yi ritaya bayan Stuttgart ta samu gurbin buga Bundesliga

Asalin hoton, Getty Images
Tsohon dan kwallon tawagar Jamus, Mario Gomez ya yi ritaya daga murza leda yana da shekara 34, bayan da ya taimakawa Stuttgart ta koma buga gasar Bundesliga.
Shi ne ya ci wa kungiyar kwallo a wasan da Darmstadt 98 ta yi nasara da ci 3-1, duk da haka Stuttgart tana mataki na biyu a teburi bai hanata kai wa gasar da za a yi a badi ba.
Stuttgard mai kofin gasar Jamus biyar ta kammala kakar bana a mataki na biyu biye da Arminia Bielefeld.
Gomez wanda shekara biyu baya ya yi ritayar buga wa tawagar Jamus kwallo wacce ya yi wa wasa 78, ya fara taka leda a Stuttgart, ya lashe Bundesliga a 2006-07.
Daga nan ya koma Bayern Munich inda ya lashe Bundesliga biyu da kofin Champions League.
Ya kuma buga tamaula a Fiorentina da Wolfsburg da kuma Besiktas daga nan ya koma Stuttgart a 2017-18.







