Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Scott McTominay: Dan wasan zai ci gaba da taka leda a Man Utd zuwa 2025
Dan kwallon Manchester United, Scott McTominay, zai ci gaba da taka leda a Old Trafford zuwa 2025 da yarjejeniyar za a iya tsawaita masa ita.
An yi wa dan kwallon wannan gatan, bayan rawar da yake takawa tun daga lokacin da ya fara wasa a kungiyar karkashin tsohon koci, Jose Mourinho.
Dan wasan tawagar Scotland mai shekara 23 ya fara buga wa United tamaula a cikin watan Mayun 2017 a fafatawa da Arsenal.
McTominay wanda aka haifa a Lancaster ya buga wasa 75 ya ci kwallo shida a gasar Premier League har da ta biyu da ya zura a ragar Manchester City a watan Maris.
Manchester United wacce take ta biyar a teburin Premier za ta karbi bakuncin Sheffield United ranar Laraba.
United ta buga 1-1 da Tottenham a gasar Premier tun da aka koma ci gaba da wasannin shekarar nan,
A cikin watan Maris aka dakatar da gasar Premier League don gudun yada cutar korona.