Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
A wane wasan za a bai wa Liverpool kofin Premier bana?
Everton za ta karbi bakuncin Liverpool a gasar Premier League karawar hamayya da za su gwabza ranar Lahadi a Goodison Park.
Wannan ne wasan farko da kungiyoyin biyu za su yi tun bayan kwana 106 da aka dakatar da gasar Premier saboda tsoron yada cutar korona.
Liverpool tana mataki na daya da maki 82, ita kuwa Everton tana da maki 37 ita ce ta 12 a kan teburin wasannin bana.
A wasan na makwabtan juna da suka yi na farko a gasar Premier a Anfield ranar 4 ga watan Disambar 2019 cin Everton 5-2 aka yi.
Wadanda suka zura wa Liverpool kwallaye Xherdan Shaqiri da Divock Origi da Sadio Mane da Georginio Wijnaldum da kuma Divock Origi da ya ci biyu.
Ita kuwa Everton ta zare kwallaye biyu n ta hannun Michael Keane da kuma Richarlison de Andrade.
Liverpool za ta iya kan-kan-kan da tarihin da ta yi a baya na yawan wasa 19 da take buge kungiya daya.
Kungiyar ta Anfield ba ta sha kashi ba a hannun Everton a wasa 21 baya da suka kara, inda ta ci 11 da canjaras 10.
Everton ba ta taba cin wasa na biyu a karawar Merseyside derby tun bayan 1987-88, a 1-0 victory at Goodison Park.
Watakila a bai wa Liverpool kofin Premier ranar 24 ga watan Yuni lokacin da za ta karbi bakuncin Crystal Palace ko kuma 2 ga watan Yuli a wasa da Manchester City.
An ci gaba da buga gasar Premier ta bana tun daga 17 ga watan Yuni ba tare da 'yan kallo ba.
Wannan wasan yana daga cikin wanda ake fargabar maogoya bayansu za su taru a wajen fili don sanin yadda karawar ke gudana.
An kuma zabi filin Southampton a matsayin ko ta kwana da kungiyoyin za su fafata da zarar an samu matsala a Goodison Park.
Wannan ne karon farko da Liverpool za ta lashe kofin Premier League tun bayan shekara 30.
Jadawalin wasannin Premier League.
Lahadi 21 ga watan Yuni
- Newcastle United da Sheffield United
- Aston Villa da Chelsea
- Everton da Liverpool
Litinin 22 ga watan Yuni
- Manchester City da Burnley
Talata 23 ga watan Yuni
- Leicester City da Brighton & Hove Albion
- Tottenham da West Ham United
Laraba 24 ga watan Yuni
- Manchester United da Sheffield United
- Newcastle United da Aston Villa
- Norwich City da Everton
- Wolverhampton Wanderers da Bournemouth
- Liverpool da Crystal Palace
Alhamis 25 ga watan Yuni
- Burnley da Watford
- Southampton da Arsenal
- Chelsea da Manchester City
Asabar 27 ga watan Yuni
- Aston Villa da Wolverhampton Wanderers
- Lahadi 28 ga watan Yuni
- Watford da Southampton
Litinin 28 ga watan Yuni
- Crystal Palace da Burnley
- Talata 30 ga watan Yuni
- Brighton & Hove Albion da Manchester United
Laraba 1 ga watan Yuli
- Arsenal da Norwich City
- Bournemouth da Newcastle United
- Everton da Leicester City
- West Ham United da Chelsea
Alhamis 2 ga watan Yuli
- Sheffield United da Tottenham Hotspur
- Manchester City da Liverpool