Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Timo Werner: Chelsea ta bai wa dan kwallon RB Leipzig yarjejeniyar shekara biyar
Chelsea ta amince ta dauko dan kwallon RB Leipzig, Timo Werner kan yarjejeniyar shekara biyar.
Dan wasan mai shekara 24 ya amince da kunshin kwantiragin da Chelsea ta gabatar masa, zai koma Stamford Bridge a watan Yuli idan an kammala Bundesliga.
Da zarar Werner ya koma Chelsea a watan gobe ba zai buga wa RB Leipzig gasar Champions League da za ta buga wasan daf da na kusa da na karshe a cikin watan Agusta ba.
Werner wanda ya koma Leipzig daga Stuttgard a 2016 ya ci kwallo 32 a dukkan fafatawar da ya yi a kakar bana.
Dan kwallon shi ne na biyu da Chelsea ta saya don shirin tunkarar kakar tamaula ta badi, bayan dan wasan Ajax, Hakim Ziyech da ta sayo a watan Fabrairu.
Chelsea wadda take ta hudu a kan teburin Premier za ta kara da Aston Villa ranar Asabar a ci gaba da gasar Premier League ta bana.
Cikin watan Maris aka dakatar da dukkan wasanni don gudun yada cutar korona.Werner ya amince da kwantiragin shekara biyar da Chelsea