Aubameyang ba ya da tabbas a Arsenal

Pierre-Emerick Aubameyang ya ce yanke shawarar ko zai sa hannu kan yarjejeniyar ci gaba da zama a Arsenal zai zama mafi mahimmaci a sana'arsa ta kwallon kafa.

A karshen watan Yunin 2021 kwantiragin dan wasan tawagar kwallon kafar Gabon zai kare a Gunners.

"Ba a gabatar min da kunshin yarjejeniya ba kawo yanzu, amma na yi magana da kungiyar a watannin baya sun kuma san dalilin da ya sa har yanzu babu abin da ya wakana," kamar yadda ya shaidawa Telefoot.

"Komai na wajen Arsenal ya rage su yi abin da ya kamata daga nan za mu san abin yi, Amma dai shawara ce mai wuyar sha'ani da zan dauka."

Aubameyang ya ci kwallo 61 a wasa 97 da ya buga wa Arsenal tun komawarsa kungiyar daga Borussia Dortmund a shekarar 2018.

A cikin watan Maris a lokacin da aka dakatar da wasanni saboda bullar cutar korona kocin Arsenal, Mikel Arteta ya ce yana son ya rike kyaftin din Gabon komai runtsi.

Ya kuma bukaci Gunners da ta tattauna da kyaftin din kan tsawaita zamansa kafin karshen kakar bana, wanda ake cewa Barcelona da Inter Milan na son yin zawarcinsa.

Arsenal wadda take ta tara a kan teburin Premier League za ta ziyarci Manchester City wadda take ta biyu a karawar da za su yi ranar 17 ga watan Yuni.