Real Madrid tana son ɗauko Sancho, Juventus ta tuntuɓi Barcelona kan aron Dembele

Asalin hoton, Getty Images
Real Madrid tana son dauko dan wasan Borussia Dortmund dan shekara 20 Jadon Sancho. (AS)
Juventus ta tuntubi Barcelona da zummar karbo aron dan wasan Faransa Ousmane Dembele, mai shekara 23, a bazara. (Mundo Deportivo - in Spanish)
Fatan kocin Manchester United Ole Gunnar Solskjaer na kara nauyin aljihun kungiyar ta hanyar sayar da dan wasan Argentina Marcos Rojo, mai shekara 30, da Chris Smalling da kuma dan wasan Chile Alexis Sanchez, mai shekara 31, zai gamu da cikas saboda rashin kudin da kungiyoyi suke fama da shi sakamakon cutar korona. (Evening Standard)
Dan wasanBournemouth Ryan Fraser, mai shekara 26, wanda ya shirya barin kungiyar don zaman aro, yana iya zama daya daga cikin 'yan wasan da kungiyoyi suka fi bukata a gasar Premier. (The Athletic - subscription only)
Paris St-Germain tana so ta karbi garin kudin da ya kai euro 175m a kan dan wasan Barcelona mai shekara 28, dan kasar Brazil Neymar. (Sport - in Spanish)
Za a bai wa masu kallo damar sauraren ihu na boge idan aka koma buga Gasar Premier. (Mirror)
Dan kasar Jamus 'Mono' Burgos, mai shekara 51, ya tabbatar da cewa zai bar mukaminsa na mataimakin koci aAtletico Madrid a karshen kakar wasa ta bana domin ya je inda zai zama koci. (Marca)
Shahararren dan kwallon Argentina Diego Maradona, mai shekara 59, zai ci gaba da zama a matsayin babban kocin kungiyar kasarsa Gimnasia y Esgrima zuwa karshen kakar wasa ta 2020-2021 bayan da aka tsawaita kwangilarsa. (Reuters)
Wani rukuni na masu goyon bayan Manchester City ya bayyana matukar bakin cikinsa a kan Uefa ranar Juma'a ta hanyar kaddamar da wani babban allo da aka rubuta kalaman da ke kyamar yadda hukumar take tafiyar da kungiyoyin kwallon kafa. (The Times)
Ana rade radin cewa Jesse Marsch, kocin Red Bull Salzburg mai shekara 46, dan kasar Amurka zai maye gurbin Lucien Favre a Borussia Dortmund. (Bild - in German).











