Coronavirus: An samu mai dauke da cutar korona a Tottenham

Tottenham training ground

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, An yi gwajin ne a wajen da Tottenham ke gudanar da atisaye

An samu mutum daya a Tottenham dauke da cutar korona a wani gwaji da aka yi kamar yadda kungiyar da ke buga Premier League ta sanar. .

Saboda haka mutumin zai killace kansa na kwana bakwai kamar yadda doka ta tanada, sannan a kara gwada shi.

Tottenham ta ce saboda matakan lafiya ba za ta bayyana sunan ko wanene ba.

Shi ne mutum na farko da aka samu dauke da annobar, bayan gwajin da aka yi wa 'yan wasa da jami'ai 1,197.

Kawo yanzu an yi zango biyar ana gwajin cutar korona ga masu hulda da wasannin Premier, inda aka samu mutum 13 dauke da annobar a gwaji 5,079 da aka yi.

Ana yi wa 'yan wasan Premier League da jami'ai gwaji sau biyu a mako a shirin da ake na ci gaba da kakar bana ranar 17 ga watan Yuni.

Ana sa ran da fara buga kwantan wasa biyu tsakanin Aston Villa da Sheffield United da na Manchester City da Arsenal.

Liverpool ce ta daya a kan teburi da tazarar maki 25 tsakaninta da Manchester City ta biyu.

Wannan ne karon farko da Liverpool za ta lashe kofin Premier League tun bayan shekara 30.

Za kuma a iya bai wa kungiyar ta Anfield kofin shekarar nan da zarar Arsenal ta yi nasara a kan Manchester City a kwantan wasan da za su buga 17 ga watan Yuni.

Tun cikin watan Maris aka dakatar da gasar Premier League don gudun yada cutar korona.