Leicester tana son ɗauko Lallana, kungiyoyi biyar na Premier suna zawarcin Coutinho

Leicester ta yi tayin bayar da kwangilar lokaci mai tsawo ga dan wasan Liverpool Adam Lallana. Kwangilar dan wasan mai shekara 32 dan kasar Ingila za ta kare a Anfield a karshen watan Yuni. (Football Insider)

Kungiyoyin Gasar Premier biyar - Chelsea, Newcastle, Manchester United, Arsenal da kuma Leicester - suna son dauko dan wasan Barcelona da Brazil Philippe Coutinho. Za a sayar da dan wasan mai shekara 27, wanda yake zaman aro a Bayern Munich, a kan £90m. (Mundo Deportivo - in Spanish)

Babu wata kungiya da ta yi tayin daukar dan wasan Real Madrid da Wales Gareth Bale don haka dan kwallon mai shekara 30 zai ci gaba da zama a kungiyar zuwa karin shekara daya. (Marca)

Manchester United da Newcastle suna son dauko dan wasan Uruguay Facundo Pellistri. A halin da ake ciki dan wasan dan shekara 18 yana buga tamaula a Penarol. (Mail)

Galatasaray tana son dauko dan wasan Bournemouth Ryan Fraser. Da ma dai ana rade radin cewa dan kasar ta Scotland mai shekara 26, wanda kwangilarsa ta kare nan gaba kadan, zai koma Arsenal ko kuma Tottenham. (Daily Record)

Everton za ta tattauna da Djibril Sidibe game da yiwuwar tsawaita zaman aron da yake yi idan aka koma buga Gasar Premier a watan Yuni. Kungiyar ta karbo aron dan kasar ta Faransa mai shekara 27 ne daga AS Monaco zuwa ranar 30 ga watan Yuni. (Liverpool Echo)

Shanghai Shenhua ta sassauta matsayinta inda ta kyale dan wasan Najeriya mai shekara 30 Odion Ighalo ya tsawaita zaman aron da yake yi a Manchester United. (ESPN)

Paris St-Germain tana dab da kammala sayen Mario Icardi. Dan kasar Argentina, mai shekara 27, yana zaman aro a PSG daga Inter Milan ko da yake wa'adin zamansa zai kare ranar 31 ga watan Mayu. (Sky Sports)

KazalikaPSG tana duba yiwuwar dauko dan wasan Chelsea dan kasar Brazil Willian. Mai yiwuwa dan wasan mai shekara 31 zai samu damar tafiya wata kungiyar don zaman aro a karshen kakar wasa ta bana. (Le10Sport - in French)

Inter Milan za ta tsawaita kwantaragin tsohon dan wasan Manchester United Ashley Young. Dan wasan mai shekara 34, ya koma kungiyar ta Italiya a watan Janairu kan yarjejeniyar wata shida. (Telegraph - subscription required)