Ranar 17 ga watan Yuni za a ci gaba da Premier League ba 'yan kallo

Ranar 17 ga watan Yuni za a ci gaba da gasar Premier League ta 2019-20 da wasa tsakanin Aston Villa da Sheffield United da na Manchester City da Arsenal.

Sauran wasannin za a ci gaba da buga su a karshen mako ne daga 19 zuwa 21 ga watan Yuni.

Saura karawa 92 a karkare gasar Premier League ta 2019-20.

Ranar 13 ga watan Maris aka dakatar da gasar Premier saboda bullar cutar korona, kuma wasan karshe da aka yi shi ne wanda Leicester City ta doke Aston Villa 4-0 ranar 9 ga watan Maris.

Ranar Labara kungiyoyin Premier suka amince da yin atisaye na bai daya tare da hada jiki, bayan da aka yi na 'yan wasa cikin rukuni ba tare da gogayya da juna ba.

An samu mutun 12 dauke da cutar korna da ke hulda da gasar Premier, bayan gwajin mutum 2,752 da aka yi.

Za kuma a ci gaba da gwajin 'yan wasa da jami'ai a duk mako biyu daga mutum 50 da ake yi a kungiya zai koma 60 nan gaba

Duk dan wasa ko jami'in da aka samu da annobar zai killace kansa na mako daya tal.

Liverpool ce ta daya a kan teburi da tazarar maki 25 tsakaninta da Manchester City, yayin da Bournemouth da Aston Villa da kuma Norwich City ke ukun karshen teburi.

Liverpool na fatan lashe kofin Premier a karon farko tun bayan shekara 30, kuma kungiyar ta Anfield za ta lashe kofin idan ta ci wasan gaba, sannan sai Arsenal ta yi nasara a kan Manchester City.