An yadda za a fitar da kungiyoyin da za su fadi da hawa gasar Ingila ta bana

An amince cewar za a samu kungiyoyin da za su fadi da wadanda za su hau gasa uku da ke kasan ta Premier League da zarar an kammala sauran wasannin da suka rage na 2019-20.

An kuma amince za a buga wasannin cike gurbi, amma kar su haura kungiyoyi hudu.

Hukumar ta English Football League ta ce ta samu kaso 51 cikin 100 daga kungiyoyin da ke buga ko Championship ko League One ko kuma League Two da suka amince a soke wasannin bana.

Hakan zai bayar da damar soke gasar League One, yayin da wasu kungiyoyin ba su da wannan ra'ayin.

A watan jiya aka kasa cimma matsaya kan tattaunawar da aka yi, bayan da wasu kungiyoyi shida da ke buga karamar gasa ta uku har da Sunderland da Portsmouth da kuma Ipswich Town suka ce suna so a ci gaba da wasannin da suka rage na bana.

Za a iya yanke matsaya ne idan dukkan kungiyoyin da ke buga Championship ko League One ko kuma League Two su 71 sun yi zaben raba gardama.

Haka kuma watakila gasar League One ta bi sahun League Two, ita ma a soke fafatawar kakar bana, bayan an gudanar da zaben.

Sai dai kuma ana fatan karkare gasar Championship, wadda ake sa ran ci gaba da wasannin kakar bana cikin watan Yuni tare da ta Premier League.

A gasar ta Premier za a fitar da wadda ta lashe kofin bana idan an karkare wasannin da suka rage da wadanda za su wakilci Ingila a gasar Zakarun Turai da wadanda za su yi ban kwana da ita.

Ranar Litinin ake sa ran 'yan wasan da ke buga Championship da na League One da na League Two za su fara yin atisaye, amma a matakan hanyoyin hana yada cutar korona.

Cikin watan Maris aka dakatar da dukkan wasanni a Ingila bayan bullar cutar korona.