Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Dortmund na goyon bayan aikin da kocinta Lucien Favre ke yi
Babban jami'in Borussia Dortmund, Hans-Joachim Watzke ya ce suna goyon bayan yadda koci, Lucien Favre ke jan ragamar kungiyar a kakar bana.
A ranar Talata ce Bayern Munich ta je ta doke Borussia Dortmund da ci 1-0 har gida a wasan mako na 28 a gasar Bundesliga.
Bayern ta ci kwallon ta hannun Joshua Kimmich saura minti biyu a je hutu, hakan ya sa Dortmund wadda ke biye da Munich an ba ta tazarar maki bakwai kenan.
An ci gaba da gasar Bundesliga a cikin watan Mayu daga wasannin mako na 27, tun bayan da aka dakatar da gasar don gudun yada cutar korona.
Tuni dai aka fitar da Dortmund daga kofin FA na Jamus da gasar Champions League a wasannin bana, watakila kocin wanda ke kaka ta biyu a bana ma ya kasa cin kofi.
Wannan ce kakar karshe da yarjejeniyar kocin na Dortmund zai kare, amma Hans-Joachim Watzke ya ce bai ga dalilin da za a dinga maganar makomar Favre ba a kungiyar.
Ya kara da cewar ''Muna buga tamaula mai kayatarwa musamman a wasannin zagaye na biyu, illa ranar Talata da aka doke mu, mun kuma samu maki 27 daga 30, mun ci wasa tara daga 10 da muka yi a baya.''
Ranar 31 ga watan Mayu Borussia Dortmund za ta ziyarci Paderborn a wasan mako na 29 a gasar Bundesliga.