Manuel Neuer: Ya tsawaita yarjejeniyar zama a Bayern Munich

Manuel Neuer ya tsawaita yarjejeniyar ci gaba da tsaron ragar Bayern Munich zuwa karshen kakar 2023.

Neuer ya lashe kofin Bundesliga bakwai da kofin kalubalen Jamus biyar da Champions League tun lokacin da ya koma kungiyar a 2011 daga Schalke.

Kyaftin din Bayern, mai shekara 34, ya buga wa tawagar kwallon kafar ta Jamus wasa 94, inda ya taka rawar gani a gasar cin kofin duniya a 2014.

Neuer zai kama gola tare da Alexander Nubel, mai shekara 23, golan Schalke wanda zai koma Bayern a farkon kakar badi.

Shi dai Neuer ya saka hannu kan yarjejeniyar shekara biyar da Bayern Munich mai rike da kofin Bundesliga.