Kasuwar 'yan ƙwallon ƙafa: Makomar Jesus, Sane, Kroos, Weghorst, Vinicius, Torreira

Asalin hoton, Getty Images
Manchester City ta shirya tsaf don sabunta kwangilar dan wasan Brazil Gabriel Jesus inda za ta rika ba shi £120,000 duk mako a yayin da rahotanni suke cewa Juventustana zawarcin dan wasan mai shekara 23. (Sun)
Sai dai a gefe daya City ta shirya sayar da Leroy Sane a bazara, duk da tsattsauran matakin da ta dauka a kanBayern Munich game da dan wasan mai shekara 24 dan kasar Jamus. Bai wuce saura wata 12 ba kwangilar Sane ta kare a City. (Evening Standard)
Dan wasan Jamus Toni Kroos, mai shekara 30, ya kawar da yiwuwar sake haduwa da Pep Guardiola a Manchester City inda ya ce yana sa ran gama sana'arsa ta kwallon kafa a Real Madrid. (Eurosport)
Dan wasan daTottenham Hotspur take son daukowa Sergej Milinkovic-Savic ba shi da niyyar barinLazio a bazara kuma za a iya yi wa dan wasan dan shekara 25 na Serbia sakayya inda za a sabunta kwangilarsa a rika ba shi £3.5m duk shekara saboda karamcin da ya yi wa kungiyar. (Corriere dello Sport via HITC)
Dan wasanWolfsburg dan kasar Netherlands Wout Weghorst ya bayyana cewa ba shi da burin buga wasa a Ingila ko da yake dan wasan dan shekara 27 ya ce Liverpool kungiya ce da yake gani a matsayin "ta musamman". (Goal)
Liverpool ta shirya dauko dan wasan Brazil dan shekara 17 Talles Magno. Matashin dan wasan, wanda ake kwatanta shi da Neymar, ya dade yana buga wasa a rukunin farko a kungiyar Vasco da Gama da ke Brazil.(Mirror)
Newcastle tana tattaunawa kan kwangilar £21.25m ta dan wasan Inter Milan Valentino Lazaro bayan dan kasar ta Austria ya taka rawar-gani lokacin da yake zaman aro a kungiyar. (Sun)
Ba a sa ranWolves ta sayo 'yan wasa a bazara duk da rahotannin da ke cewa ta ware £53m don sayo dan wasan Benfica dan kasar Brazil Carlos Vinicius, mai shekara 25. (Express and Star)
Wakilin dan wasan tsakiya naArsenal Lucas Torreira ya yi ikirarin cewa dan wasan dan shekara 24 yana son barin Emirates Stadium domin ya koma Italiya. (Tuttomercatoweb via Metro)
Tsohon kocin Arsenal Unai Emery ya yi ikirarin cewa an tilasta masa dauko Nicolas Pepe, mai shekara a Arsenal - inda ya bayyana cewa da so samunsa ne, da ya dauko Wilfried Zaha, mai shekara 27, bayan ya tattauna da fitaccen dan wasan na Crystal Palace. (Mail)
Real Madrid tana ci gaba da son dauko Erling Braut Haaland kuma za ta sanya ido kan dan wasan mai shekara 19 ranar Asabar lokacin da Borussia Dortmund za ta koma buga gasar Bundesliga. (Mundo Deportivo - in Spanish)
Chelsea ta shirya sayar da manyan 'yan wasa da dama domin samun kudin gudanar da harkokinta a bazara amma ana sa ran za ta ki amsa tayin sayar da N'Golo Kante, dan shekara 29, da kuma Jorginho, dan sekara 28. (ESPN)
Leicester City ba za ta yi musayar Wilfred Ndidi idan aka bude kasuwar musayar 'yan kwallon kafa ba a yayin da ake rade radin Paris St-Germain da Manchester Unitedsuna zawarcin dan wasan na Najeriya. (All-Nigeria Soccer)
Barcelona tana ci gaba da yunkurin dauko dan wasan Bayer Leverkusen Kai Havertz. Ana hasashen cewa dan wasan mai shekara 20 zai koma Liverpool amma har yanzu Barca bata hakura da yunkurin dauko shi ba. (Sport1 - in German)










