Faransa: An soke dukkan wasannin kwallon kafa na Ligue 1 da 2

PSG players celebrate a goal against Dijon in Ligue 1

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, PSG tana kan gaba a teburi da tazarar maki 12 da kwantan wasa daya

Ba za a kammala gasar Faransa ta Lique 1 da 2 ta bana ba, bayan da gwamnati ta dakatar da dukkan wasanni har da wanda babu 'yan kallo har karshen Satumba.

Firai Minista, Edouard Philippe ya ce dukkan wasannin kakar 2019-20 an soke su, bayan da yake sanar da shirin da Faransa ke yi na janye dokar hana fita daga 11 ga watan Mayu.

Mahukuntan kwallon kafar Faransa sun so a ci gaba da gasar Faransa ranar 17 ga watan Yuni a kuma karkare ranar 25 ga watan Yuli.

A ranar 13 ga watan Maris aka dakatar da dukkan wasannin tamaula a Faransa saboda tsoron yada cutar korona.

Sai dai mahukuntan gasar League din Faransa ba su fayyace ko an karkare wasannin bana ba tare da kungiyoyin da za su fadi da wadanda za su maye gubinsu ba.

Ko kuma za ta yi amfani da gurbin da kungiyoyin ke kai kawo wannan lokacin.

Mai rike da kofi Paris St Germain ce ke kan gaba da maki 12 tsakaninta da Marseille ta biyu, kuma saura wasa 10 da kwantai daya a kare kakar 2019-20.