Lyon ta bai wa Juventus mamaki a Faransa

Champions League

Asalin hoton, Getty Images

Juventus ta yi rashin nasara da ci 1-0 a Lyon a wasa farko zagaye na biyu a gasar Champions League.

Lucas Tousart ne ya ci kwallon tun kan su je hutu, kuma karo na biyu da Lyon ta ci kungiyar ta Italiya karawa biyar da suka yi.

Sai dai sau uku Juventus na doke Lyon a gasar ta zakarun Turai.

Juventus ta zura kwallo a raga, daga baya alkalin wasa bai karba ba da cewar an yi satar gida.

Juventus ce kan gaba wajen rike kwallo a wasan, amma ta kasa ratsa bayan Lyon, hasali ma ba ta buga kwallon da ya hufi raga kai tsaye ba.

Lyon za ta ziyarci Juventus a wasa na biyu ranar 17 ga watan Maris da za su fafata a Allianz Stadium.