Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Coronavirus: Za a yi bincike kan yada cuta a wasan Liverpool da Atletico
Magajin garin Liverpool ya yi kira da a yi bincike ko wasan da Liverpool ta yi da Atletico yana da alaka da yada cutar korona a gasar Champions League da suka yi 11 ga watan Maris.
Sama da 'yan kallo 52,000 suka kalli karawar da aka yi a Anfield har da mutum 3,000 magoya bayan Atletico daga Spaniya garin da aka hana zirga-zirga a wasu wuraren saboda hana yada cutar korona.
Gwamnatin Burtaniya ce ta amince a buga wasan daga baya ta sa dokar hana fita kwana 10 tsakani da yin fafatawar.
Ana son yin binciken ne don tabbatar da ko wasan na Champions League da aka buga a Anfield yana da alaka da yada cutar a birnin Liverpool.
Kimanin mutum 246 ne suka mutu a Liverpool a asibiti sakamakon kamuwa da annobar.
Haka kuma birnin Madrid shi ne garin da aka fi samun yawan wadanda suka mutu sakamakon cutar a Spaniya kasa ta biyu a duniya da mutane da dama suka mutu bayan Amurka.
An kuma bukaci yin bincike kan ko gasar sukuwar dawaki ta bikin Cheltenham da aka yi a Maris ita ma tana da alaka da yada cutar korona.
Ana fargabar yana daga cikin dalilan da ya sa aka samu karuwar masu dauke da cutar, bayan da 'yan kallo 251,684 suka kalli gasar da aka yi kwana hudu ana gabatarwa.