Za a jingine biyan albashin 'yan Premier

Kungiyoyin Premier da wadanda ke buga Football League za su yi taro ranar Laraba da kungiyar kwararrun 'yan wasan tamaula kan jingine albashi zuwa wani lokaci.

Wannan yana daga cikin tsarin taimaka wa kungiyoyin Ingila da suke fuskantar tattalin arziki saboda coronavirus.

Haka kuma kungiyar kwararrun 'yan wasan kwallon kafar za ta tambayi kungiyoyin da ke buga wasannin Ingila ko wannan tsarin zai yi kyau da bukatunsu.

An tsayar da gasar cin kofin Premier Ingila wadda ake sa ran ci gaba da fafatawa ranar 30 ga watan Afirilu, saboda bullar annoba.

Sai dai wasu na ganin nan gaba kadan komai zai koma yadda aka saba, sannan a karkare wasannin kakar bana.

Ranar 18 ga watan Maris mahukuntan gasar League a Ingila suka ce za su biya fam miliyan 50, domin taimaka wa kungiyoyin da suka samu gibi wajen biyan albashi sakamakon dakatar da wasannin.

Taron da za su gudanar ranar Laraba zai mayar da hankali kan yadda za a magance bukatun watan Afirilu na kungiyoyin.