Dan wasan Juventus Matuidi ya kamu da coronavirus

Juventus

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Matuidi na cikin tawagar Faransa da ta lashe kofin duniya a 2018

An gwada dan wasan tsakiya na Juventus Blaise Matuidi an ga ya kamu da cutar coronavirus.

Kungiyar ta ce dan wasan Faransan ya kebe kansa tun 11 ga watan Maris kuma "lafiya lau ba tare da nuna alamun cutar ba"

Matuidi mai shekara 32, shi ne dan wasa na biyu a kungiyar da aka tabbatar yana dauke da cutar, bayan dan wasan dake buga baya a kungiyar Daniele Rugani.

Tuni dai aka dakatar da duka wasanni a Italiya har sai 3 ga watan Afrilu.