An jinkirta gasar French Open zuwa karshen shekara

Roland Garros

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Gasar ta French Open ita ce ta biyu da ake gudanar wa ko wacce shekara bayan Australian Open.

An matsar da Gasar Tennis ta French Open zuwa watan Satumba da Oktoban shekarar nan da muke ciki saboda coronavirus.

Gasar ta Roland Garros ana gudanar da ita ne daga 24 ga watan Mayu zuwa 7 ga watan Yunin kowacce shekara, amma yanzu za ta gudana ne tsakanin 20 ga watan Satumba zuwa 4 ga watan Oktoba.

Hakan yana nufin za a fara gasar mako guda bayan kammala US Open a New York.

An dakatar da duk wata gasar kwararru ta Tennis yanzu a duniya har sai ranar 20 ga watan Afrilu.

Gasar ta French Open ita ce ta biyu da ake gudanar wa ko wacce shekara, bayan Australian Open da ake fara gudanar wa.