Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Arsenal ta kai zagayen gaba a FA Cup
Arsenal ta doke Portsmouth da ci 2-0 a wasan zagaye na biyar a gasar FA Cup da suka kara ranar Litinin.
Arsenal ta fara cin kwallo ta hannun Sokratis Papastathopoulos daga baya Eddie Nketiah ya kara na biyu.
Da wannan sakamakon Arsenal ta kai wasan daf da na kusa da na karshe a FA Cup.
Arsenal ta buga karawar bayan da Olympiakos ta fitar da ita daga gasar Zakarun Turai ta Europa League ta bana ranar Alhamis.
Koci Mikel Arteta ya yi sauye-sauyen 'yan wasa, inda ya saka mai tsaron baya Pablo Mari, wanda karon farko ya fara buga wa Gunners tamaula.
Dan wasan Arsenal Lucas Torreira ya ji rauni a karawar, bayan ketar da James Bolton ya yi masa, hakan ya sa aka fitar da shi daga filin wasa.
Kawo yanzu ta doke Portsmouth sau 22 a jere, rabon da ta yi rashin nasara da kungiyar tun kakar 1958.
Wannan kofin na FA ne ya ragewa Gunners a bana da take harin dauka, bayan da Chelsea wadda take ta hudu ta bai wa Arsenal tazarar maki takwas a gasar Premier.
Arsenal wadda take kan gaba wajen Lashe FA Cup mai guda 10, sai dai kuma rabon da ta ci kofin tun kakar 2016/17.
Manchester City ce mai rike da kofin bara.
Wasannin da za a buga ranar Talata 3 ga watan Maris.
- Chelsea da Liverpool
- West Bromwich Albion da Newcastle United
- Reading da Sheffield United