Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Liverpool: Henderson zai yi jinyar mako uku
Kocin Liverpool, Jurgen Klopp, ya ce kyaftin dinsu Jordan Henderson zai yi jinyar mako uku sakamakon raunin da ya ji a cinyarsa a karawar da suka yi da Atletico Madrid.
An tilasta wa Henderson, mai shekara 29, fita daga wasa gabanin a kammala karawar da Liverpool ta doke Madrid da ci 1-0.
Dan wasan na tsakiya ya yi wa kungiyar wasa sau 34 a kakar wasa ta bana, inda ya ci kwallaye uku.
"Mun samu labarin 'yan wasan da suka yi fama da rauni a cinyarsu a gasar Firimiya - alal misali, Harry Kane - amma nasu bai yi tsanani ba," a cewar Klopp ranar Juma'a.
An yi wa dan wasan Tottenham Kane- takwaran wasan Henderson a Ingila - tiyata a cinyarsa ranar daya ga watan Janairu kuma ana sa ran zai koma atisaye a watan Afrilu.
Klopp ya kara da cewa: "[Henderson] zai yi jinyar mako uku ko kusan haka, kuma bamu ji dadi ba, sai dai duk da haka mun yi sa'a."
Cikin makonni uku masu zuwa, Liverpool za su fafata a gasar Firimiya da West Ham United, Watford da kuma Bournemouth, yayin da kuma za su buga zagaye na biyar na wasan cin kofin FA da Chelsea, da kuma wasa da Atletico na 'yan 16 a gasar Zakarun Turai.