Cikin minti uku Arsenal ta gama da Newcastle

Arsenal ta hada maki uku a kan Newcastle United, bayan da ta ci 4-0 a wasan mako na 26 da suka fafata a Emirates ranar Lahadi.

Tun farko kungiyoyin sun je hutu ba tare da kwallo ya shiga raga ba.

Sai bayan da suka koma zagaye na biyu ne Arsenal ta kara kaimi ta zura kwallo biyu a raga kuma cikin minti uku.

Pierre-Emerick Aubameyang ne ya fara zura mata kwallo a minti na tara da komawa wasa, sannan minti uku tsakani Nicolas Pepe ya kara na biyu.

Daf da za a tashi wasan ne Mesut Ozil ya kara na uku a raga, sannan Alexandre Lacazette ya ci na hudu

Arsenal za ta karbi bakuncin Everton a wasan mako na 27 a gasar ta Premier ranar 23 ga watan Fabrairu a Emirates.