'Man City za ta ba mu wuya saboda hukuncin dakatarwa'

Kocin Real Madrid, Zinedine Zidane yana tsammanin kwarin gwiwar da Manchester City ke da shi yanzu zai iya "bai wa Madrid matsala" yayin karawarsu ta Champions League.

Hukumar kwallon kafar Turai Uefa ce dai ta dakatar da Man City daga shiga gasannin nahiyar Turai na shekara biyu, abin da ke nufin dole ne City ta yi bakin kokarinta ta lashe na bana.

City ta ce za ta daukaka kara kuma kwana 10 kacal gare ta domin yin hakan. An kama kungiyar da laifin keta dokokin kashe kudade.

"Abokan hamayyar za su ba mu wuya matuka," Zidane ya bayyana.

Ya kara da cewa: "Ganin irin abin da ya faru da su, kwarin gwiwar da suke da shi a yanzu mai yawa ne."

Real da City za su fafata a filin wasa na Bernebeu a wasan zagayen 'yan 16 ranar 26 ga watan Fabarairu, sai kuma a yi wasa na biyu a Etihad ranar 17 ga Maris.

"Ba sai na fadi me ya faru ba ko kuma abin da zai faru," in ji Zidane.

"Kulob ne da zai ba mu wuya sosai ganin yadda suke taka leda a Premier. Saboda haka yanzu suna da kwarin gwiwa na musamman."

City ba ta taba wuce wasan kusa da na karshe ba a Champions League, kuma ba su taba kwata fayinal ba a karkashin Guardiola.

Kocin ya bayyana a kwanakin baya cewa idan har bai lashe gasar ba to za a bayyana zamansa a kungiyar a matsayin "gazawa".

Sai dai lashe Champions League ya fi wa City sauki sama da Premier, yayin da take bin Liverpool da tazarar maki 22.