Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Dembelen Barcelona zai yi jinyar wata shida
A ranar Talata likitoci suka yi wa Ousmane Dembele aiki kan raunin da ya ji a kafarsa, sun kuma ce zai yi jinyar wata shida.
Likitan da ya ja ragamar aiki, Dakta Lasse Lempainen ya ce raunin ya yi muni, kum,a shi ne ya yi masa aiki a wanda ya yi wata hudu kan ya koma taka leda a 2017.
Karo na uku kenan da Dembele ke jin rauni da yake jinya mai tsawo tun komawarsa Barcelona a 2017.
Barcelona ta dauki dan kwallon Borussia Dortmund, Ousmane Dembele kan kudin da ake cewa ya kai sama da fam miliyan 135.
Hakan ya sa dan kwallon ya zama na biyu mafi tsada a duniya a tarihin tamaula da aka saya a lokacin, bayan Neymar da ya koma Paris St-Germain kan fam miliyan 200 daga Barcelona.
Dembele ya yi wa Barcelona wasa tara a kakar bana, inda ya ci mata kwallo daya a fafatawa da ta ci Seville 4-0 ranar 16 ga watan Oktoba.