Man Utd sun rage farashin Pogba, Arsenal za su sayar da Aubameyang da Lacazette da Ozil

Asalin hoton, Getty Images
Manchester United ya rage £30m kan farashin da ya sanya ga duk kulob din da ke son sayen dan wasan tsakiya na Faransa Paul Pogba, mai shekaru 26, wanda za a kyale shi ya tafi idan aka biya £150m. (Sun)
Kazalika an cire Pogba daga cikin 'yan wasan Manchester United da za su yi balaguro zuwa Spain. (Star)
Kocin Arsenal Mikel Arteta yana shirin yi wa tawagarsa garambawul, inda ake sa ran zai tallata dan wasan Gabon Pierre-Emerick Aubameyang, mai shekara 30; dan wasan Faransa Alexandre Lacazette, mai shekara 28; da kuma tsohon dan wasan tsakiya na Jamus Mesut Ozil, mai shekara 31. (Sun)
Barcelona na shirin sayen dan wasan Wolves Adama Traore, mai shekara 24, a lokacin bazara. (Mail)
Dan wasan Inter Milan dan kasar Argentina Lautaro Martinez, mai shekara 22, ba zai yarda da tayin da Manchester City da Manchester United suka yi masa ba na koma daya daga cikinsu a bazara mai zuwa, kuma maimakon hakan zai tafi Barcelona.(Star)
Manchester United sun fasa yin zawarcin Martinez saboda £94m da aka bukaci su biya kafin dan kasar ta Argentina ya koma kulob din. (Times - subscription required)
Leicester City na zawarcin dan wasanLiverpool da Ingila Adam Lallana. Su ma Tottenham, Arsenal da West Ham na son sayen dan wasan mai shekara 31. (Telegraph)
Mai tsaron ragar Ajax dan kasar Kamaru mai shekara 23, Andre Onana,ya ce ya fi so ya komaChelsea a bazara mai zuwa, a yayin da Chelsea ke duba yiwuwar maye gurbin dan kasar Spain Kepa Arrizabalaga, mai shekara 25. (Goal.com)
Everton sun fasa zawarcin dan wasan Everton Soares, mai shekara 23, duk kuwa da ikirarin da dan wasan Gremio dan kasar Brazil ya yi cewa Kocin Everton Carlo Ancelotti da dan wasan Brazil Richarlison suna tattaunawa kan batun. (Liverpool Echo)
Manchester United ba zai karbi "kasa da £15m ba" wajen cefanar da dan wasan Ingila Chris Smalling, mai shekara 30. (Team Talk)











